Esdras 2
La liste de ceux qui revinrent
Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu. 2Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana). Ga jerin mazan mutanen Isra’ila. 3Zuriyar Farosh mutum 2,172 4ta Shefatiya 372 5ta Ara 775 6ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,812 7ta Elam 1,254 8ta Zattu 945
9ta Zakkai 760 10ta Bani 642 11ta Bebai 623 12ta Azgad 1,222 13ta Adonikam 666 14ta Bigwai 2,056 15ta Adin 454 16ta Ater (ta wurin Hezekiya) 98
17ta Bezai 323 18ta Yora 112 19ta Hashum 223 20ta Gibbar 95.
21Mutanen Betlehem 123 22na Netofa 56 23na Anatot 128 24na Azmawet 42 25na Kiriyat Yeyarim, da Kefira Beyerot 743 26na Rama da Geba 621 27na Mikmash 122 28na Betel da Ai 223
29na Nebo 52 30na Magbish 156 31na ɗayan Elam ɗin 1,254 32na Harim 320 33na Lod, da Hadid da Ono 725 34na Yeriko 345 35na Sena’a 3,630.
36Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 973 37ta Immer 1,052 38ta Fashhur 1,247 39ta Harim 1,017.
40Lawiyawa. Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodawiya) mutum 74. 41Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 128. 42Masu tsaron haikali. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai mutum 139.
43Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot, 44Keros, Siyaha, Fadon, 45Lebana, Hagaba, Akkub, 46Hagab, Shamlai, Hanan, 47Giddel, Gahar, Reyahiya, 48Rezin, Nekoda, Gazzam, 49Uzza, Faseya, Besai, 50Asna, Meyunawa, Nefussiyawa,
51Bakbuk, Hakufa, Harhur, 52Bazlut, Mehida, Harsha, 53Barkos, Sisera, Tema, 54Neziya da Hatifa.
55Zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda, 56Ya’ala, Darkon, Giddel, 57Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Ami.
58Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392. 59Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba. 60’Yan zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 652.
61Daga cikin firistoci kuma, zuriyar Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna). 62Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne. 63Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna.
64Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360, 65ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200. 66Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245, 67raƙuma 435, da jakuna 6,720.
Des dons pour la maison de Dieu
68Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake. 69Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100. 70Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu.