诗篇 129
他们屡次苦害我
Waƙar haurawa. Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce, 2sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba. 3Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi.
4Amma Ubangiji mai adalci ne; ya ’yantar da ni daga igiyoyin mugaye. 5Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya. 6Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma; 7da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.
8Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”
已复制!
Aa