Salmi 61

Conducimi sulla roccia più alta di me

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Ta Dawuda. Ka ji kukata, ya Allah; ka saurari addu’ata. 2Daga iyakar duniya na yi kira gare ka, na yi kira yayinda zuciyata ta karai; ka bishe ni zuwa dutsen da ya fi ni tsayi. 3Gama kai ne mafakata, hasumiya mai ƙarfi gāba da maƙiyi.

4Ina marmari in zauna a tentinka har abada in sami mafaka a cikin inuwar fikafikanka. Sela 5Gama ka ji alkawarina, ya Allah; ka ba ni gādo na waɗanda suke tsoron sunanka. 6Ka ƙara kwanakin ran sarki, shekarunsa su kasance a zamanai masu yawa.

7Bari yă yi mulki a gaban Allah har abada; ka sa ƙaunarka da amincinka su tsare shi. 8Sa’an nan zan riƙa rera yabo ga sunanka in kuma cika alkawarina kowace rana.

Copiato!
Aa