Salmi 11
Nel Signore mi rifugio
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don busa. Ta Dawuda. A wurin Ubangiji ne nake samun mafaka. Yaya za ku ce mini, “Ka yi firiya kamar tsuntsu zuwa duwatsu. 2Gama duba, mugaye sun tanƙware bakkunansu; sun kuma ɗana kibiyoyinsu don su harbi mutanen kirki a zuciya daga cikin duhu. 3Sa’ad da aka tumɓuke tushe, me adali zai iya yi?” 4Ubangiji yana cikin haikalinsa mai tsarki; Ubangiji yana a kursiyinsa a sama. Yana kallon ’ya’yan mutane; idanunsa suna bincike su.
5Ubangiji yana bincike adalai, amma ransa yana ƙi mugaye da masu son rikici. 6A kan mugaye zai zuba garwashin wuta mai zafi da kuma kibiritu; iska mai zafi zai zama rabonsu. 7Gama Ubangiji mai adalci ne, yana ƙaunar gaskiya masu adalci za su ga fuskarsa.
Copiato!
Aa