Salmi 102
La preghiera dell'afflitto
Addu’ar mutum mai shan wahala. Sa’ad da ya rasa ƙarfi ya kuma yi makoki a gaban Ubangiji. Ka ji addu’ata, ya Ubangiji; bari kukata ta neman taimako ta zo gare ka. 2Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni sa’ad da nake cikin damuwa. Ka juye kunnenka gare ni; sa’ad da na yi kira, ka amsa mini da sauri. 3Gama kwanakina sun ɓace kamar hayaƙi; ƙasusuwana suna ƙuna kamar jan wuta.
4Zuciyata ta kamu da ciwo ta kuma bushe kamar ciyawa; na manta in ci abinci. 5Saboda nishina mai ƙarfi na rame na bar ƙasusuwa kawai. 6Ni kamar mujiyar jeji ne, kamar mujiya a kufai.
7Na kwanta a faɗake; na zama kamar tsuntsun da yake shi kaɗai a kan rufin ɗaki. 8Dukan yini abokan gābana suna tsokanata; waɗanda suke mini ba’a suna amfani da sunana yă zama abin la’ana. 9Gama ina cin toka a matsayin abincina ina kuma gauraye abin sha nawa da hawaye 10saboda fushinka mai girma, gama ka ɗaga ni sama ka yar a gefe.
11Kwanakina suna kamar inuwar yamma; na bushe kamar ciyawa. 12Amma kai, ya Ubangiji, kana zaune a kursiyinka har abada; sunan da ka yi zai dawwama a dukan zamanai. 13Za ka tashi ka kuma ji tausayin Sihiyona, gama lokaci ne na nuna alheri gare ta; ƙayyadadden lokacin ya zo.
14Gama duwatsunta suna da daraja ga bayinka; ƙurarta kawai kan sa su ji tausayi. 15Al’ummai za su ji tsoron sunan Ubangiji, dukan sarakunan duniya za su girmama ɗaukakarka. 16Gama Ubangiji zai sāke gina Sihiyona ya kuma bayyana a ɗaukakarsa.
17Zai amsa addu’ar marasa ƙarfi; ba zai ƙyale roƙonsu ba. 18Bari a rubuta wannan don tsara mai zuwa, cewa mutanen da ba a riga an halitta ba za su yabi Ubangiji, 19“Ubangiji ya duba ƙasa daga wurinsa mai tsarki a bisa, daga sama ya hangi duniya, 20don yă ji nishe-nishen ’yan kurkuku yă kuma saki waɗanda aka yanke musu hukuncin mutuwa.” 21Saboda haka za a furta sunan Ubangiji a Sihiyona yabonsa kuma a Urushalima 22sa’ad da mutane da mulkoki suka tattaru don su yi wa Ubangiji sujada.
23Cikin rayuwata, ya karye ƙarfina; ya gajartar da kwanakina. 24Sai na ce, “Kada ka ɗauke ni a tsakiyar kwanakina, ya Allah; shekarunka suna bi cikin dukan zamanai. 25A farkon fari ka kafa tushen duniya, sammai kuma aikin hannuwanka ne.
26Za su hallaka, amma za ka ci gaba; duk za su tsufe kamar riga. Kamar riga za ka canja su za a kuwa zubar da su. 27Amma kana nan yadda kake, kuma shekarunka ba za su taɓa ƙarewa ba. 28’Ya’yan bayinka za su zauna a gabanka; zuriyarsu za su kahu a gabanka.”