Salmos 3

Muchos se levantan contra mí

Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni! 2Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” Sela 3Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.

4Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. Sela 5Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni. 6Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.

7Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye. 8Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. Sela

¡Copiado!
Aa